in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwararrun kasar Sin sun isa Conakry
2014-08-12 15:30:26 cri
Kwararrun kasar Sin sun isa a ranar Litinin a Conakry domin taimakawa kasar Guinea kan kokarin da take na yaki da cutar Ebola, da kasar ke fama da ita tun farkon wannan shekara da kuma tuni ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 367 daga cikin mutane 495 da aka gano suna dauke da cutar.

Tawagar likitancin ta kasar Sin na kunshe da wani masanin cututtuka masu yaduwa, masanin cututtuka da kuma masanin kiyaye mutane daga kamuwa da cututtuka.

Kwararrun na kasar Sin sun isa Conakry a rana guda da zuwa jirgin sama kirar Boejing 747 dake dauke da ton 80 na kayayyakin likitanci da magunguna. Kuma an mikawa hukumomin Guinea ton 24 yayin da sauran kayayyakin za'a wuce da su zuwa Liberiya da Saliyo. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China