in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masanan kiwon lafiya na Sin na kan hanyar zuwa kasashe uku dake yammacin Afirka
2014-08-10 20:38:03 cri
A daren Lahadin nan ne ake fatan wasu kwararru a fannin kiwon lafiya na kasar Sin, za su tashi daga nan birnin Beijing, zuwa kasashen Guinea, da Liberia da kuma Saliyo. Yayin da kuma ake sa ran wata tawagar ta daban, za ta tashi zuwa wadannan kasashe a gobe.

Rahotanni daga taron horaswa na masana kiwon lafiyar da aka gudanar kafin tashin wannan tawaga, sun nuna cewa tawagogin na kasar Sin na wannan karo, za su hadu da tawagogin da kasar ta tura kasashen uku a baya, don musayar kwarewa game da hanyoyin magance yadunar cutar Ebola.

Kaza lika tawagogin za su nazarci halin da ake ciki yanzu haka a kasashen, domin shirya gudanar da ayyukansu yadda ya kamata. An kuma ce tawagogin za su taimaka wa ofisoshin jakadancin kasar Sin dake kasashen uku wajen samar da kayayyakin agajin da kasar Sin ta samar musu, za su kuma horas da masanan kasashen dabarun amfani da kayayyakin agajin.

A wani ci gaba kuma, kayayyakin agaji da kasar Sin ta aike zuwa kasashen yammacin Afirka da suka fi fama da cutar Ebola a halin yanzu, sun riga sun bar birnin Shanghai na nan kasar Sin da yammacin Lahadin, ana kuma sa ran isar su kasashen nan da ranar 11 zuwa ta 12 ga wata. Wadannan kayayyakin agaji dai sun hada da tufafin kariya, da magungunan kawar da kwayoyin cuta, da wasu magunguna masu alaka da dai sauransu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China