Ban Ki-moon ya bayyana hakan ne a gun taron manema labaru da aka gudanar a cibiyar MDD a jiya Talata. Ya kuma ce hadin kai tsakanin kasa da kasa domin shawo kan wannan cuta yana da muhimmancin gaske wajen tinkarar ta.
Nadin Nabarro dai ya biyo bayan ganawar da Mr. Ban ya yi da babbar direktar hukumar WHO Margaret Chan. Nabarro dai masani ne a fannin harkokin kiwon lafiya na WHO, ya kuma taba zama jami'i mai kula da cutar murar tsuntsaye na MDD.
Yayin tabbatar da nadin nasa, Mr. Ban Ki-moon ya kara da cewa, aikin farko da ake fatan zai gudanar shi ne, warware matsalar rashin karfin ikon tinkarar cutar da kasashen Guinea, da Liberia da Saliyo ke fuskanta, duba da cewa kasashen ba su jima da farfadowa daga rikice-rikicen siyasa ba.
Kaza lika Ban Ki-moon ya yi kira ga kasashen duniya, da su bada tasu gudummawa game da matsalar rashin isassun likitoci, da tufaffin bada kariya, da tantuna da sauran na'urori da ake bukata a wadannan kasashe, yana mai cewa kamata ya yi jama'a su yi watsi da tsoron cutar ta Ebola. (Zainab)