Ministan lafiya na Najeriya Onyebuchi Chukwu ya ce, lamari na baya-bayan nan shi ne na wata nas da ta yi cudanya da Patrick Sawyer, dan kasar Liberian nan da ya mutu a Najeriya sanadiyar cutar.
Ministan ya shaidawa manema labarai a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya cewa, bayan gwajin da aka yi wa ma'aikaciyar a karshen mako, yanzu daga ranar Jumma'a zuwa yau Litinin, an kara samun mutum guda da ya kamu da cutar, adadin da ya kai mutane 10 ke nan.
A ranar Jumma'ar da ta gabata ce shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ayyana dokar ta baci, tare da ware Naira biliyan 1.9 don kare yaduwar cutar.
Ya zuwa yanzu cutar ta Ebola ta halaka sama da mutane 900 a kasashen yammacin Afirka. (Ibrahim)