in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Asibitoci a Liberiya sun koma bakin aikin su bayan barkewar cutar Ebola
2014-08-08 21:02:07 cri
Rahotanni daga Monrovia babban birnin kasar Liberiya na nuna cewa asibitoci sun koma bakin aikin su bayan barazanar barkewar cutar Ebola ya sa sun dakatar da aiki makonnin da suka gabata kamar yadda Gwamnatin kasar ta tabbatar.

Ministan yada labarai na kasar Lewis Brown ya shaida ma manema labarai a Monrovia cewa babban asibitin gwamnati na tunawa da John F Kennedy ya fara gudanar da ayyukan shi a sashin kula da marasa lafiya na gaggawa.

Ya yi bayanin cewa wani asibitin Redemption shi ma na gwamnatin inda wani likitan dan asalin kasar Uganda da wata ma'aikaciyar jinya wato Nas suka mutu sakamakon wannan annoba ta Ebola shima a yau jumma'an nan zai koma bakin aiki ma marasa lafiyan da ba za'a kwantar da su ba sannan ya zuwa litinin mai zuwa a fara aiki gadan gadan.

Har ila yau Sojojin kare kasar na Liberiya sun fara jibge jami'an su a wurare daban daban na kasar don taimakawa wajen yin bincike a wuraren cinkoson jama'a da kuma lura da zirga zirgan al'umma a kasar.

Ministan tsaron kasar Brownie Samukai a don haka ya bukaci al'ummar kasar dasu tsaya a wuraren da suke da nufin hana yaduwar wannan annoba. (Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China