A cikin sanarwar, Jonathan ya bukaci makarantu da su tsawaita wa'adin hutawa bisa yanayin da ake ciki, kuma ya bukaci jama'ar kasar da kada su gaskata jita-jita dangane da cutar Ebola tare da yin kira ga mutanen kasar dasu kiyaye magance shiga cikin taron jama'a, da kaucewa jigilar gawawwaki daga ketare zuwa Nijeriya.
Gwamnatin kasar ta riga ta bukaci ma'aikatar kiwon lafiya da hukumar kyautata harkokin gaggawa ta kasar Nijeriya da sauransu da su hada gwiwa wajen daukar matakai tare domin yaki damagance yaduwar cutar a Nijeriya. Haka kuma, shugaban ya yi kira ga jama'ar kasar da su maida hankali wajen sfahimtar cutar Ebola, domin yaki da yaduwarta bisa iyakacin kokarinsu.
A jiya kungiyar WHO ta bayyana a birnin Geneva cewa, yaduwar cutar Ebola a wuraren dake yammacin Afirka ta riga ta kasance batun kiwon lafiya da kasa da kasa ke mai da hankali a kai. Bisa sabon rahoton da kungiyar WHO ta bayar kan cutar Ebola, an ce, zuwa ranar 4 ga wata, baki daya yawan mutanen da suka kamu da cutar Ebola, da watakila sukawadanda ake tababarsu da kamuwa da cutar Ebola ya kai 1711 a Guinea da Liberia da Sierra Leone da kuma Nijeriya, a kuma cikinsu mutane 932 suka mutu. Dadin dadawa, tun daga ranar 25 ga watan Yuli da aka gano mutum na farko da ya kamu da cutar Ebola da ya fito daga Liberiya zuwa Nijeriya zuwa yanzu, an riga an samu mutane 9 da watakila sukaake shakkarsu da kamuwa da cutar Ebola, a ciki mutum dayayayin da daya daga cikinsu tya rasu.(Fatima)