Wata sanarwar da ma'aikatar ta fitar a baya bayan nan ta ce, an samu rahotanni dake tabbatar da wasu masunta, dake kamun kifi a wasu wurare masu makwaftaka da kasar Laberiya sun kamu da wani nau'in ciwo mai kama da cutar ta Ebola.
Don haka ne ma'aikatar lafiyar ta bukaci daukacin al'ummar kasar da su shiga taitayinsu domin kaucewa barkewar wannan annoba a kasar.
A cewar hukumar wajibi al'umma su kauracewa shiga wuraren wanka na al'umma, tare da kara kula da tsaftar muhalli da sauran hanyoyin kiwon lafiya kamar yawaita wanke hannaye.
Sanarwar ta kara da cewa, duba da cutar kwalara da ta barke a wasu sassan kasar ta Ghana, da kamanceceniyar da take da ita da cutar Ebola, ya zama wajibi al'umma su kauracewa taba gawar mutanen da suka rasu da hannayensu, su kuma rika sanya safar kariya idan za su taba marasa lafiya.
Hukumar ta lafiya ta kuma ba da lambobin waya na musamman domin mika sakwannin ko-ta-kwana, da zarar an ji alamun wata cuta da ba a amince da ita ba, duka dai da nufin kare barkewar cutar Ebola a kasar. (Saminu)