Jami'in wanda ya bayyana hakan jiya a birnin Nairobi, ya kara da cewa babban sakataren ma'aikatar kiwon lafiyar kasar Fred Segal, ya bayyanawa mahalarta wani taron tattaunawa game da hanyoyin hana yaduwar cutar ta Ebola cewa, a halin yanzu, kasashen dake gabashin nahiyar Afirka suna gudanar da hadin gwiwa a kan iyakokinsu, domin hana yaduwar cutar.
Haka zalika a cewarsa gwamnatocin kasashen sun karfafa matakan kandagarki, da na jan hankulan al'umma, tare da sayo kayayyakin binciken cutar da dai sauransu.
Bugu da kari, Mr. Segal ya kara da cewa, kasashen gabashin Afirka na mai da hankali sosai kan yanayin yaduwar cutar ta Ebola. (Maryam)