Kayayyakin agajin kasar Sin za su isa kasashe uku dake fama da Ebola a ranar litinin 11 ga wata
A yau Jumma'a 8 ga wata, rahotanni daga hukumar bincike kan kayayyakin shigi da fici ta birnin Shanghai ta sanar da cewa, ma'aikatan jirgin saman da za su dauki nauyin jigilar kayayyakin agajin jin kai na kasar Sin zuwa kasashe uku na yammacin nahiyar Afirka wadanda ke cikin yanayi mai tsanani wajen tinkarar annobar Ebola, wato su Guinea,Liberia,da Saliyo, sun riga sun kammala daukan horo na yadda zasu shawo kan cututtuka. A sabili da haka, an yi kiyasin cewa, kayayyakin ba da jiyya mai nauyin ton 80 za su isa kasashen uku na yammacin Afirka a ranar litinin 11 ga watan nan na Agusta.(Fatima)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku