A lokacin ganawar Wang Yi ya bayyana cewa, a kokarin da bangarorin biyu suke yi, taron ministoci karo na shida na dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da kasashen Larabawa ya samu ci gaba sosai saboda a taron shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tsai da shirin da bangarorin biyu za su bi wajen yin hadin gwiwa da hanyar da za a bi nan gaba. Ministan yace wannan ya baiwa dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu makoma mai kyau a cikin shekaru 10 masu zuwa. Don haka in ji shi ya kamata, bangarorin biyu sun dauki matakai da suka dace domin tabbatar da ci gaban da aka samu a taron.
A nashi bangare, Nabil el-Araby ya lura da cewa, Sin ta kan bin hanyar adalci da daidaici, kuma tana goyon bayan ayyuka masu kyau da kasashen Larabawa suke yi, abin da ya nuna cewa, Sin sahihiyar abokiya ce ga kasashen Larabawa wadda suke iya dogaro da ita. (Amina)