in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin MDD ya jinjinawa shawarar kafa sabuwar jihar tsakiyar Somalia
2014-07-31 10:01:10 cri

Wakilin musamman na babban magatakardar MDD a kasar Somalia Nicholas Kay, ya yi maraba da yarjejeniyar kafa sabuwar jihar yankin tsakiyar kasar Somalia.

Hakan, a cewar Kay, wani muhimmin mataki ne da ya dace da manufofin da ake fatan cimmawa nan da shekarar 2016, karkashin tanaje-tanajen kundin mulkin kasar.

Kay wanda ya bayyana hakan ta bakin kakakin MDD Stephane Dujarric, ya kuma ce, MDD a shirye take, ta goyi bayan duk wani yunkuri na wanzar da zaman lafiya da lumana a Somalia.

A ranar Laraba ne dai kusoshin gwamnatin tarayyar kasar, da wakilan yankuna, suka rattaba hannu kan wasu kudurori masu alaka da kafuwar sabuwar jihar tsakiyar kasar. Zaman da ya samu halartar manyan wakilai daga kungiyoyin yankuna da na kasa da kasa, ciki hadda da AU da kuma MDD. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China