Zaunannen wakilin kasar Rasha dake MDD Vitaly Churkin ya bayyana a ran 28 ga wata a birnin New York hedkwatar MDD cewa, Rasha na kin yarda da duk wani matakin da aka dauka domin baiwa kungiyar adawa da gwamnatin kasar Sham matsayin kungiyar kasashen duniya.
Vitaly Churkin ya ce, kungiyar kasa da kasa ta kasance kungiya dake kula da harkokin tsakanin gwamnatocin kasashen duniya, bai kamata ba a baiwa kungiyar adawa wadda ba ta samu amincewa bisa hanyar shari'a ba wannan matsayi. Ya kara da cewa, kungiyar AL ta yanke shawarar baiwa kungiyar adawa ta kasar Sham matsayin mamba na kungiyar, abin da ta yi ya sabawa kokarin da kasa da kasa suke yi na warware rikicin kasar cikin hanzari, tare kuma da karya kokarin da wakilim musamman na MDD da kungiyar AL Lakhdar Brahimi ya yi. Ban da haka, ya ce, matakin da kungiyar AL ta dauka ba ma kawai ya kawo barazana ga matsayinta, har ma ya kawo babbar illa ga kokarin da ake yi na warware rikicin kasar Sham.
An ba da labari cewa, an kira taron shugabannin kungiyar AL karo na 24 a ran 26 ga wata a birnin Doha hedkwatar kasar Qatar, inda aka yanke shawarar baiwa kungiyar adawa da gwamnatin kasar Sham ta SNCORF matsayin mambar kungiyar AL. (Amina)