in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sake kai harin boma-bomai a yankin Gaza bayan dokar tsagaita bude wuta ta fara aiki
2014-08-01 20:20:45 cri
Hukumar kiwon lafiya ta Falesdinu ta gaskata a yau 1 ga watan Agusta cewa, bayan da dokar tsagaita bude wuta ta sa'o'i 72 ta fara aiki, sojojin Isra'ila sun sake kai harin boma-bomai a kudancin yankin Gaza, wanda ya haddasa mutuwar Falesdinawa guda hudu. Wannan ya sa ita ma, kungiyar Hamas ta harba makaman roka kudancin kasar Isra'ila don mai da martani.

Bisa labarin da sojojin tsaron kasar Isra'ila suka bayar, an ce, an harba rokoki sama da guda 20 daga yankin Gaza zuwa kasar Isra'ila bayan dokar tsagaita bude wuta ta fara aiki. Sai dai kafofin watsa labarai na kasar Isra'ila, sun ce, sojojin tsaron kasar Isra'ila sun sanar wa MDD game da kawo karshen dokar tsagaita bude wuta sabo da hare-haren da Hamas ta kai mata. Amma rundunar sojin kasar Isra'ila ta ki yiwa manema labarai bayani kan lamarin.. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China