Manyan batutuwan dake cikin sanarwar Doha, su ne, tabbatar da ba da damar kasance mambar kungiyar AL ga kungiyar 'yan adawar kasar Syria, tare da yin kira ga sauran kungiyoyin kasa da kasa da su amince da matsayin 'yan adawar kasar Syira, kuma sanarwar ta baiwa mambobin kasashen kungiyar AL izinin samar da makamai ga kungiyar adawar Syria, ita kuma ta yi kira ga bangarorin daban daban da abin ya shafa da su warware matsalar Syria ta hanyar siyasa. Haka zalika sanarwar ta fidda wani shirin kiran taron farfado da kasar Syria, inda aka yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su bai wa jama'ar Syria taimakon kudi, a sa'i daya kuma, sanarwar ta yi kira ga kasashen Larabawa da su ci gaba da yaki da kasar Isra'ila, kana ta yi kira ga kasashen Larabawa da su kara karfafa cudanya tsakanin gwamnatoci da jama'a.
A yayin taron, tsohon shugaban kungiyar 'yan adawar kasar Syria Mouaz Al-Khatib ya yi kira ga MDD da sauran kungiyoyin kasa da kasa da su mika kujerun kasar Syria nasu ga kungiyar, tare da neman a rike kudade da kadarorin gwamnatin dake karkashin jagorancin Bashar al-Assad domin amfani da su wajen gina kasar. (Maryam)