in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD ya yi kira da a fidda sahihin tsarin aiwatar da sulhu a Mali
2014-07-29 09:57:16 cri

Kwamitin tsaron MDD ya yi kira ga daukacin sassan kasar Mali, da su jajirce wajen tabbatar da sahihin tsarin sulhu, wanda ake kokarin cimmawa tsakanin masu ruwa da tsaki a kasar.

Kwamitin tsaron dai ya yi fatan dukkanin bangarori, za su goyi bayan shirin wanzar da daidaito da ake fatan nasarar sa, wanda ya hada da amincewa da gudanar da karin muhimman shawarwari, tun daga ranar 17 ga watan Agusta mai zuwa a birnin Aljiyas na kasar Aljeriya.

Hakan a cewar wakilan kwamitin na tsaro, zai ba da damar tattauna batutuwan da ke da tasiri matuka, ga shirin wanzar da zaman lafiya tsakanin daukacin al'ummun arewacin Mali, da nufin shawo kan matsalar rarrabuwar kawuna dake zamewa kasar babbar barazana.

An dai gudanar da zaman tattaunawa tsakanin sassan masu ruwa da tsaki a Mali a karon farko ne, tsakanin ranekun 16 zuwa 24 ga watan Yulin nan, zaman da kuma ya samar da zarafin gudanar da shawarwari tsakanin tsagin gwamnati da na 'yan awaren Azbinawa masu tada kayar baya. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China