Taron da ya samu halarta a kalla shugabannin kasashen Larabawa 15 sun hada da shugaban kasar Masar Mohamed Morsi, sarkin Qatar Sheikh Hamad bin Khalifa Al-Thani da kuma shugaban al'ummar Palestinu Mahmoud Abbas.
Moaz al-Khatib, shugaban kungiyar 'yan adawa na kasar Sham mazauna kasashen waje da ya yi murabus shi ne ya zauna a kan kujerar wakilin Damascus, kuma ana sa ran zai gabatar da jawabinsa a lokacin wannan taro.
Shi dai wannan taro na kwanaki biyu shi ne na 24 tun kafuwar kungiyar, wanda a da ake kiran shi gamayyar kasashen Larabawa lokacin da aka kafa shi a shekarar 1945.
Mataimakin shugaban kasar Iraqi Khudeir Musa Al Khuza tun da farko a cikin jawabinsa ya yi kira ga kungiyar da ta kafa wani kwamitin tsaro da zai warware wannan matsala da ake fuskanta na tashin hankali a kasar ta Sham.(Fatimah)