in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Sin ya gana da sakatare janar na kungiyar AL
2014-01-24 10:54:27 cri
A jiya Alhamis 23 ga wata, a birnin Montreux dake kasar Switzerland, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gana da sakatare janar na kungiyar tarayyar kasashen Larabawa AL wato Nabil el-Araby.

Wang Yi ya ce, bana shekara ce ta cika shekaru 10 da kafa dandalin hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa, kuma za a yi taron ministocin harkokin waje da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa karo na 6 a nan kasar Sin, abun da ke da muhimmanci sosai game da raya dandalin hadin gwiwa da ke tsakanin bangarorin biyu. Nan gaba, ya kamata bangarorin biyu su kara inganta mu'amala da shawarwari, don ba da tabbaci ga shirya taron lami lafiya.

Wang Yi ya ce, bayan da bangarorin daban daban suka yi kokari, an yi taron Geneva karo na 2 game da batun Siriya, kuma kasashen duniya sun cimma matsaya guda, amma bangarori biyu na Siriya suna ci gaba da yin fito-na-fito da juna, kuma ana fuskantar matsaloli da dama. Ya kamata kungiyar AL ta kara taimakawa a wajen shawarwarin. Kasar Sin ba ta da wata moriyar kanta game da batun Siriya, abin da take sanya muhimmanci a kai shi ne kiyaye zaman lafiya a wannan shiyya da kuma moriyar kasashe masu tasowa ciki har da kasashen Larabawa. Nan gaba, kasar Sin za ta ci gaba da ba da gudummawa ta fannin sassauta matsalar jin kai a kasar.

Araby ya ce, kasar Sin, babbar kasa ce da kasashen Larabawa suke amincewa da ita. Dandalin tattaunawar hadin gwiwa da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa, wani taron tattaunawa ne da aka shirya cikin nasara, sabo da haka, kasashen Larabawa suna fatan ci gaba da inganta hadin gwiwa da kasar Sin, don ba da tabbaci ga shirya taron tattaunawa karo na 6 kamar yadda aka tsara.

A nasa bangare kuma, Araby ya ce, duk da cewa, ana fuskantar matsaloli da dama game da batun Siriya, amma ya kamata a ci gaba da yin shawarwari.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China