Bugu da kari, babban magatakardan MDD Ban Ki-moon ya ba da wata sanarwa a ran 1 ga wata cewa, take yarjejeniyar tsagaita bude wuta a yankin Gaza ta bata masa rai sosai, don haka, ya yi alla wadai da dukkanin matakan da aka dauka wadanda suka janyo rashin girmama yarjejeniyar da aka cimma, ya kuma yi kira ga Falesdinu da Isra'ila da su dukufa wajen kai zuciya nesa, a sake dawo yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta sa'o' i 72 da aka kulla a baya, ya kuma yi kira ga bangarorin daban daban na gamayyar kasa da kasa da su ba da taimako wajen ciyar da tsagaita bude wuta a yankin Gaza gaba.
Haka zalika, shugaban kasar Amurka Barack Obama ya bayyana a jiya Jumma'a cewa, Amurka ta yi allawadai da farmakin da dakarun Falesdinu suka kai kan sojojin Isra'ila bayan fara aikin yarjejeniyar tsagaita bude wuta a wannan rana. (Maryam)