An gudanar da wani taron na musamman game da manufar samar da makamashi ta hanyar bola, taron da ya zamanto irinsa na farko, wanda kuma a ka yiwa lakabi da "Kowa na da ikon mallakar makamashi na bola jari".
Taron na yini uku ya gudana ne a birnin New York hedkwatar MDD. Ya kuma samu halartar babban magatakardan MDD Mr. Ban Ki-Moon, da wakilin musamman na taron Kandeh Yumkella, da sauran wakilai fiye da 1000 daga gwamnatoci, da sashen masana'antu da kasuwanci, da kungiyoyin kasa da kasa, da kuma kungiyoyi masu zaman kansu.
Yayin zaman taron, mahalartansa za su tattauna da kimanta alkawarin da kasashe daban daban suka yi kan yadda suka baiwa dukkan sassan duniya damar amfani da makamashi na bola jari. Kuma za a nuna wasu kyawawan misalai da matakan kirkire-kirkire a wannan fanni, domin baiwa bangarori daban-daban kwarin gwiwar karfafawa manufofinsu game da makamashi nan da shekaru fiye da goma masu zuwa.
Dadin dadawa, an fitar da wani rahoto kan halin da makamashi na bola jari ke ciki a duniya a shekarar 2014, inda aka nuna cewa, kasashe masu saurin ci gaban tattalin arziki, wadanda suka rungumi manufar amfani da makamashi na bola jari ya ninka har sau 6 cikin shekaru 8 da suka gabata, wato yawan irin wadannan kasashe ya karu daga 15 a shekarar 2005 zuwa 95 a farkon shekarar bana.
Bugu da kari rahoton ya bayyana cewa, kasashen Sin, da Amurka, da Brazil, da Canada da Jamus, suna sahun gaba a fannin jimillar na'urorin samar da lantarki bisa makamashin bola jari, inda a karon farko wannan jimilla da Sin ta samu ta zarce ta hanyar amfani da kwal, man fetur, iskar gas da kuma nukiliya. (Amina)