Mahukuntan kasar Afirka ta Kudu, sun alkawarta baiwa shirin tsaron makamashi dukkanin goyon bayan da ya dace, yayin taron tsaron makamashi na duniya, da za a bude yau Litinin 24 ga wata a birnin Hague.
Wata sanarwa daga ma'aikatar lura da huldar kasa da kasa ta Afirka ta Kudun ce ta tabbatar da hakan. Sanarwar ta kuma ce, ministan ma'aikatar Maite Nkoana-Mashabane ne zai jagoranci tawagar kasar domin halartar taron.
Har wa yau, sanarwar ta ce, taron na bana zai baiwa Afirka ta Kudun damar bayyana manyan manufofinta a wannan fanni, da suka hada da burinta na kwance makaman nukiliya, da hana saduwar su, tare da tabbatar da takaita amfani da makamashin nukiliya a harkokin farar hula kadai.
Ana dai sa ran taron na yini biyu, zai dora inda aka tsaya a baya, game da tattauna ci gaban da aka samu, tun bayan makamancin sa na shekarar 2010. Baya ga kudurin tabbatar da tsaron nukiliyar ta hanyar hadin gwiwar kasashen duniya.
Bugu da kari gabanin bude taron na bana, Nkoana-Mashabane zai jagoranci ganawar da ministocin wajen kasashe mambobin kungiyar BRICS za su yi. (Saminu)