Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe a jiya Talata 23 ga wata a garin Dubai na hadaddiyar daular kasashen Larabawa ya ce, an shirya tsarin da ake bi yanzu na samar da makamashin iskar gas na duniya, don haka ya yi kira ga kasashen Afrika da su hada kansu domin samar da tsarin samar da makamashi mai cin gashin kai ga nahiyar.
Lokacin da yake jawabi mai taken makamashi na Afrika a taron kwanaki uku na makamashi na duniya a shekara ta 2012 da ake yi a Dubai, Mugabe ya ce, "Afrika, nahiyarmu mai hasken rana tana da dinbin albarkatun kwal da kuma gwargwadon makamashin iskar gas da mai wanda zai iya zama wani katafaren cibiya na samar da makamashin hasken rana. Amma a madadin haka, Afrika tana fitar da yawancin albarkatunta na mai da kayayyaki zuwa wassu kasashen duniya. Ya kamata mu sake juyawa baya domin mu yi amfani da albarkatunmu masu daraja wajen samar da wutar lantarki ga al'ummarmu."
Shugaba Mugabe ya kara da cewa, muhawaran da ake yi yanzu game da yadda za'a samar da makamashi ma mutane biliyan 2 wadanda ba su da halin amfani da wutar lantarki, "an sa siyasa a ciki matuka" ba tare da an yi nuni musamman ga kasashe ko kungiyoyi ba.
"Siyasa ba ya da matsugunni a irin wadannan batutuwa masu taba zukata." in ji Mugabe, yana mai kira ga gwamnatoci a nahiyar da su hada hannu da karfe domin samar da wutar lantarki mai tsabta, musamman ga talakawa dake zaune a kauyukan nahiyar.(Fatimah)