Mnistan makamashi da man fetur na kasar Ghana Emmanuel Armah-Kofi, yana ziyarar aiki a kasar Sin, da nufin kara janyo masu zuba jari a bangaren makamashin kasar.
Yayin ziyarar ministan a nan kasar Sin, ana sa ran zai ziyarci wasu cibiyoyin makamashi, inda zai gana tare da yin musayar ra'ayoyi da wasu manyan masu ruwa da tsaki a bangaren na makamashi a kasar ta Sin, wadanda suka hada da manyan kamfanonin samar da wutar lantarki da ke Shanghai da kuma Shenzhen, wato iyayen gidan kamfanin samar da wutar lantarki na Suno-Asogli da ke Ghana.
Wata sanarwar da ma'aikatar makamashi da man fetur ta kasar Ghana ta bayar a ranar Litinin na nuna cewa, ministan zai tattauna da jami'an wadannan kamfanonin biyu da nufin zakulo hanyoyin fadada kamfanonin samar da wutar lantarkin da ke Ghana. (Ibrahim)