An kira babban taron makamashi na kasa da kasa karo na 22 a jiya Lahadi 13 ga wata a birnin Daegu na kasar Korea ta kudu, inda mahalarta taron suka tattauna kan kwaskwarimar da za a yi wa sha'anin makamashi, tsare-tsare da manufofi dangane da wannan fanni, kana su kai ga cimma matsaya daya wajen fitar da tsarin daidaita wasu matsaloli.
Taron na wannan karo mai taken "Tabbatar da isashen makamashi nan gaba" ya samu halartar kwararru kan makamashi, manyan jami'ai, jiga-jigan kamfannoni kimanin 6000, daga cikinsu akwai ministoci ko mataimakan ministocin makamashi.
Taron wanda za a kammala a ranar 17 ga wata, ya kasance mafi girma da amfani a duniya a wannan fanni. (Amina)