Kasar Ghana ta bayyana fatanta a ranar Talata na ba da hadin gwiwa cikin kungiyar makamashi ta MDD tsakanin kasashe masu tasowa wato Kudu da Kudu (SSEI).
Cibiyar MDD kan hadin gwiwar Kudu da Kudu (UNOSSC) ta kafa kungiyar SSEI bayan wata bukatar kasashen dake fitar da man fetur da gas dake kudancin duniya.
Ghana ta dauki niyyar dukufa a cikin wannan kungiya, kamar yadda ta yi a cikin sauran kungiyoyi makamantan haka da suka hada da kungiyar kasashen 'yan ba ruwanmu, tarayyar Afrika (AU) da kungiyar Commonwealth domin ganin mambobin SSEI su ma sun samu tagwamashin harakar arzikin ma'adinansu na man fetur da gas domin cigaban kasashensu.
Ministan makamashin kasar Ghana, Emmanuel Armah-Koff Buah ya ba da tabbatancin kasarsa a yayin wani zaman aikin kaddamar da reshen shiyya na SSEI a kasar Ghana.
Kasar Ghana ta amince da wannan kungiya a cikin watan Yulin da ya gabata ta hanyar karbar cibiyar SSEI a kasarta.
SSEI kungiya ce mai zaman kanta, ta kasa da kasa dake mai da hankali kan bukatun duniya, da masu fada a ji na kudancin duniya suka kafa kuma suke tafiyar da harkokinta ta hanyar hedkwatarta dake birnin Accra na Ghana. (Maman Ada)