Gwamnatin kasar Cote d'Ivoire ta dauki niyya a ranar Alhamis ta kafa cikin gaggawa wasu kamfanonin gwajin samar da sabbin makamashi domin fuskantar kalubalolin dake da nasaba da muhalli dalilin gurbacewar yanayi.
Kakakin gwamnatin kasar Cote d'Ivoire, mista Bruno Kone ya ba da wannan sanarwa bayan wani taron ministoci.
Mista Bruno Kone ya bayyana cewa, ta wannan mataki, gwamnati na fatan fuskantar kalubalolin dake nasaba da dumamar yanayi da kuma matsalar hauhawar farashin makamashi kasar kamarsu man fetur da wutar lantarki. Niyyar gwamnati ita ce ta bullo da wasu sabbin hanyoyin maye gurbin wadannan makamashi.
Kamfanonin gwajin za'a kafasu a biranen Man a yammaci, Korhogo a arewaci, Bouake a tsakiya da Bouna a arewa maso gabashin kasar tare da taimakon gwamnatin kasar Cote d'Ivoire da hadin gwiwar cibiyar ayyukan birni ta kasar Jamus wadda ita ce za ta samar da horo ga kwararrun wadannan biranen da za'a baiwa nauyin shugabantar kamfanonin a nan gaba. (Maman Ada)