in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan majalisun kungiyar ECOWAS na taro kan matsalar makamashi mai tsabta kuma a farashi mai rahusa a yammacin Afrika
2012-12-05 10:27:08 cri

Yan majalisun kungiyar ECOWAS sun fara wani taro tun ranar Talata kan matsalar makamashi mai tsabta kuma a farashi mai rahusa da zai taimaka wajen tallafawa cigaban tattalin arziki da na al'umma a cikin wannan kungiya mai kunshe da kasashe goma sha biyar a wani labarin da cibiyar kamfanin dillancin labarai na Xinhua dake birnin Lome na kasar Togo ta samu.

Zaman taron na kwanaki biyar ya hada da 'yan majalisu na kwamitin hadin gwiwar gine-gine, cigaban masana'antu, noma, muhalli, albarkatun ruwa da kuma cigaban karkara. Kuma mahalartan za su mai da hankali kan batun makamashi bisa taken 'samar da makamashi mai tsabta kuma a farashi mai rahusa domin cigaban tattalin arziki da na al'umma a cikin kasashen kungiyar ECOWAS'.

Hakazalika taron na Lome zai bai wa 'yan majalisu damar samun bayanai kan cigaban da aka samu wajen kaddamar da aiwatar da tsare-tsaren ayyukan dake da nasaba da makamashi mai tsabta kuma a farashi mai rahusa a wannan shiyya ta yammacin Afrika.

A cewar 'yan majalisun, yammacin Afrika na fama da karamcin makamashin wutar lantarki dake kasancewa makulli ko tushe ga duk wani cigaban tattalin arziki da na al'umma, kuma ko akwai makamashi yana da tsada, tare da jaddada cewa, Allah ya albarkanci yammacin nahiyar Afrika da albarkatun makamashi masu dimbin yawa, musammun ma na hasken rana, man fetur da gas.

Rashin makamashi na kasancewa wani babban kalubale dake hana cigaban tattalin arziki da na al'umma a shiyyar yammacin Afrika, in ji mataimakiya ta biyu ta shugaban majalisar dokokin kasar Togo madam Ouro-Bang'na Nassara. (Maman ADA)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China