Shugaban kamfanin Sonatrach, Abdelhamid Zerguine ya bayyana cewa, a halin yanzu, an gudanar da bincike kan dukkan matakan tsaron da za a dauka don kyautata su, kuma za su cika alkawarin daukar matakan, da zarar an tabattar da dacewarsu bisa doron dokokin kasar.
Ya kuma kara da cewa, babban dalilin da ya sa masu tsattauran ra'ayin suka iya kai wa mahakar iskar gas ta Tiguentourine farmaki a tsakiyar watan Janairun da ya gabata, shi ne rashin masu gadi masu dauke da makamai, shi ya sa, Zerguine ya bayyana cewa, kamfanin a yanzu haka na burin sanya masu gadi da za su yi amfani da makamai, da zarar sun samu amincewar tanadin doka, da a yanzu haka suka mika bukata a kan ta.
A ranar 16 ga watan Janairu ne dai wasu dakaru masu alaka da kungiyar al-Qaida, suka kai wa mahakar iskar gas din dake Tiguentourine a birnin Amenas farmaki, a yankin dake kudu maso gabashin babban birnin kasar wato Algiers, sa'annan suka yi garkuwa da ma'aikata kimanin 800 'yan kasashe daban daban, kafin daga bisani sojojin kasar su ceto galibi daga cikinsu. (Maryam)