Rahoton ya ce, a shekarun da suka gabata, kasar Sin ta kara yin kokarin daukar matakai don tinkarar matsalar sauye-sauyen yanayi. A shekarar 2012, kasar Sin ta zuba jari na dala biliyan 65.1 wajen raya makamashi mai tsabta, wanda ya kai kashi 30 cikin kashi dari na adadin kudin da kungiyar G20 ta zuba a wannan fanni, kana ya fi na kasar Amurka wato dala biliyan 35.6. Kana rahoton ya nuna yabo ga kasar Sin domin ta yi kokarin cika alkawari sosai wajen tinkarar matsalar sauye-sauyen yanayi.
Hukumar kula da harkokin yanayi ta kasar Australia hukuma ce da gwamnatin kasar, hukumar nazari kan kimiyya da masana'antu ta kasar da kuma jami'ar Melbourne suka zuba jari wajen kafa ta. Wannan rahoton da hukumar ta gabatar ya bayyana yadda ake tinkarar matsalar sauye-sauyen yanayi a fadin duniya, kana ya sa lura kan ci gaban da Sin da Amurka suka samu wajen tinkarar matsalar. (Zainab)