in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya za ta kammala sanya bangaren makamashinta kasuwa a watan Yuli
2013-06-06 14:00:26 cri

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana a ranar Laraba cewa, za ta kammala aikin sanya bangaren makamashinta kasuwa nan da watan Yuli domin baiwa 'yan Najeriya kusan miliyan 120 damar samun wutar lantarki.

Sakatariyar kasa kan makamashi, Zainab Kuchi ta yi wannan sanarwa ga manema labarai bayan wani taron mako mako na kwamitin zartaswa na tarayya (FEC) a birnin Abuja.

Mutane miliyan 40, suke amfani da wutar lantarki bisa mutane miliyan 160 dake cikin wannan kasa, in ji madam Kuchi.

Sayar da bangaren makamashi zai kammala a cikin watan Yuli. Sannan abun da za mu mai da hankali a kai shi ne kasuwancin bangaren makamashi, idan aka yi la'akari cewa, kashi 40 cikin 100 na wutar lantarki kawai muke samarwa 'yan Najeriya, in ji madam Kuchi. Haka kuma ta jaddada cewa, ma'aikatarta ta dauki alkawarin samarwa 'yan Najieriya wutar lantarki nan da 'dan gajeren lokaci, tare da nuna cewa, wannan aiki na bangaren makamashi zai kawo alheri sosai ta fuskar kudin shiga da riba ga bangaren hakar man fetur, idan ana kasuwancinta yadda ya kamata.

A nasa bangare, ministan makamashin Najeriya Chinedu Nebo ya bayyana cewa, Najeriya ta wuce sarrafa megwatt 2500 na wutar lantarki zuwa megawatt 4000. Burinmu shi ne na kai ga megawatt 10000 nan da shekarar 2014. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China