in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mozambique za ta zuba jari a fannin makamashi mai tsafta
2014-05-06 10:08:22 cri

Gungun masana 'yan kasar Mozambique dake ketare, da takwarorin su dake cikin kasar sun fara wani taron lalubo hanyoyin raba kasar da gurbatar muhalli, sakamakon amfani da makamashi mai illa ga muhallin.

Rahotanni daga kasar na cewa, kwararrun da tuni suka fara taron na su a birnin Maputo, helkwatar kasar a jiya Litinin, za su nazarci hanyoyin samarwa kasar makamashi mai tsafta, tare da rage yawan makamashi mai gurbata muhalli da kasar ke sayowa daga ketare.

Da yake karin haske game da wannan batu, mataimakin minista a ma'aikatar makamashin kasar Jaime Himede, cewa ya yi, makamashin da ake samarwa daga tsirrai na da matukar muhimmanci ga Mozambique, don haka ne ma kasar ke karfafa gwiwar manomanta, wajen samar da nau'o'in amfanin gona, da ake iya fidda sinadaran samar da makamashi daga gare su.

Mozambique dai na fatan koyi da kasar Brazil, wadda tuni ta yi nisa wajen rage gurbata muhalli ta hanyar fidda iska mai gurbata muhalli, bayan da ta samu nasarar bunkasa sarrafa rake a matsayin hanyar samar da makamashi. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China