in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Ghana za ta bunkasa makamashin nukiliya
2013-07-04 10:59:27 cri

Ministan makamashi da man fetur na kasar Ghana ya tabbatar da kafa wasu matakai da dokoki domin bunkasa makamashin nukiliya.

A cewar wata sanarwar ofishin wannan minista, wani daftarin kafa wata hukumar kula da wannan aiki mai zaman kanta, da aka tsara domin gina tashar samar da makamashin nukiliya ya isa majalisar dokokin kasar domin samun amincewa.

Ministan makamashi da man fetur na Ghana, Emmanuel Armah-Kofi Buah ya bayyana cewa, bukatun dake karuwa kan wutar lantarki a cikin kasar na bukatar gaggauta kafa matakai da dokoki domin fara aikin samar da makamashin nukiliya, tare da kara bayyana cewa, lokaci ya yi a duba hanya sosai.

Tare da kafa tsarin doka da na daidaitawa, gudanar da bincike wajen zaben wurin gina tashar, kammala bincike kan kayayyakin aiki da tattalin arziki, da shirye-shiryen neman kudaden da za su fara wannan shekara, muna kusanto wa ga gina tashar makamashin nukiliya ta farko a kasar Ghana. in ji mista Buah.

Ministan ya dawo Ghana bayan ya halarci wani taron ministoci kan makamashin nukiliya a wannan karni na 21 a makon da ya gabata da hukumar makamashi ta duniya (IAEA) ta shirya a kasar Rasha.

An yi shawarwari sosai tsakanin hukumar makamashin nukiliya ta kasar Rasha, ROSATOM da ministan makamashi da man fetur na kasar Ghana a yayin wannan taro kan batutuwan da suka shafi bangarorin biyu da za su taimaka wajen aiwatar da shirin kasar Ghana na bunkasa wata tashar makamashin nukiliya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China