Hukumar makamashi ta duniya (WEC) ta bayyana ranar Talatar nan cewa, yayin da batun karancin makamashi da kuma batun bunkasar tattalin arziki a nahiyar Afirka suka zamo abubuwa masu jan hankali, masu zuba jari a nahiyar daga kasar Sin da Indiya za su taka muhimmiyar rawa a masana'antar makamashi don shawo kan matsalar makamashi a nahiyar.
A cikin wani rahoto da aka samar yayin babban taro kan makamashi a Afirka da aka gabatar a birnin Johannesburg, mai taken 'sa ido kan batutuwan makamashi a duniya' hukumar ta WEC ta bayyana cewa, muhimman manufofi da za su iya jan hankalin masu zuba jari zuwa nahiyar Afirka a fannin makamashi na da muhimmanci matuka.
Rahoton ya ci gaba da cewa, koma bayan tattalin arziki a duniya da kuma karancin makamashi dukka suna shafar bukatun samar da wutar lantarki a nahiyar Afirka.
Hukumar ta ci gaba da cewa, tana mai nuna goyon baya ga masu tsara manufofi a fadin duniya a kokari da suke na bullo da manufofi da za su janyo masu zuba jari a wannan fanni da kuma kawo daidaito.(Lami)