in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala kashi 80 bisa dari na aikin samar da makamashin iskar methane a Rwanda
2014-05-27 14:23:20 cri

Ministan makamashi na Rwanda Emma Francoise Isumbingabo ya ce, an kammala kashi 80 bisa dari na aikin samar da makamashin iskar methane, wacce ke gundumar Karongi.

Ministan wanda ya bayyana hakan a jiya Litinin a yayin da yake ziyarar aikin tare da shugaban bankin raya kasashen Afrika Donald Kaberuka ya kuma ce, ana sa rai tashar za ta fara gudanar da aiki a watan Satumba mai zuwa.

Ministan ya kara da cewar, a kalla za'a kara karfin wutar lantarki na kasar da megawatts 25 daga bangaren iskan methane a watan Satumba.

Rwanda na kokarin tabbatar da kashi 70 bisa dari na mutanen kasar, an hada su da wutar lantarki nan da shekara ta 2017.

Kashi 18 ne kawai bisa dari na mutanen Rwanda suke samun wutar lantarki a yanzu, kuma bankin raya kasashen Afrika ne ya dauki nauyin wani bangare na gina tashar wutar lantarkin, kuma bankin kawo ya zuwa yanzu ya kashe dalar Amurka miliyan 180 a kan aikin da ake yi. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China