in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan makamashin da ake amfani da shi a kasar Sin ya kasance matsayi na biyu a duniya
2012-09-03 16:20:13 cri

Kwanan baya, hukumar nazarin makamashin kasar Sin ta bayar da wani rahoto a birnin Beijing inda aka bayyana cewa, bisa sakamakon kididdigar da kasar Amurka da kasar Sin suka samu, an ce, kwatankwacin yawan makamashin da ake amfani da shi a kasar Sin ya kai matsayi na biyu a duniya, amma adadin ma'auni da ko wane mutum ke amfani da shi, ya kai matsakaicin matsayi ne kawai a duniya.

Rahoton ya nuna cewa, a shekarar 2011, yawan makamashin da aka yi amfani a kasar Sin ya kai nauyin kwal tan miliyan 3478, ya karu da kashi 7 cikin dari idan aka kwatanta shi da na shekarar 2010, hakan ya kai matsayi na biyu ne a duniya.

Ban da wannan kuma, an ce, yawan makamashin da ko wane basine ya yi amfani da shi a shekarar 2011 kimanin kwal tan 2.59 ne kawai wanda ya kai matsakaicin matsayi kawai a duniya. Haka zalika, ko da yake kwatankwacin yawan makamashin da kasar Sin ta yi amfani da su ya kai kashi 20 cikin dari na duk daukacin makamashin da kasa da kasa ke amfani da su, amma, duk da haka, yawan jama'ar kasar Sin ya kai kashi 20 cikin dari na daukacin jama'ar duk fadin duniya, shi ya sa, matsayin kasar Sin na amfani da makamashi bai kai na kasashen Amurka, Japan, Korea ta kudu da sauran kasashen duniya ba.

Yanzu a kasar Sin, kwal ya kasance makamashi mafi muhimmanci, kasar Sin ita ma kasa ce mai arzikin kwal, saboda haka, kasar Sin tana da kashi 90.5 cikin dari na makamashi a cikin gida, kuma yawansu ya ragu bisa kashi 0.86 cikin dari idan aka kwatanta shi da na shekarar 2010.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China