in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD da bankin duniya na shirin fidda tsarin bunkasa samar da makamashi
2013-11-28 10:19:22 cri

MDD da hadin gwiwar babban bankin duniya sun bayyana aniyar hada karfi da karfe, domin bunkasa sashen samar da makamashi ga daukacin al'ummar duniya.

Babban magatakardar MDDr Ban Ki-moon, da shugaban bankin duniya Jim Yong Kim ne, suka bayyana hakan yayin ganawarsu da manema labaru, bayan kammalar wata tattaunawa da wakilan sashen ba da shawarwari na shirin samar da makamashi ga kowa, da ya gudana a ranar Laraba 27 ga wata.

Cikin jawabinsa, Mr. Ban ya yi kira ga gwamnatoci, da hukumomin kasa da kasa, da kungiyoyin al'umma da su yi namijin kokari, wajen bunkasa samar da kudaden gudanar da ayyuka a wannan sashe. Ban ya ce, samar da ingantaccen makamashi jigo ne na bunkasar tattalin arziki, da kyautatuwar rayuwar jama'a, wanda kuma ke taimakawa ga samuwar managarcin muhallin rayuwa ga dan adam.

A nasa tsokaci, Kim cewa ya yi, samar da isassun kudade muhimmin mataki ne na bunkasa makamashi, don haka ya bukaci da a samar da kudaden da yawansu ya kai tsakanin dala biliyan dari shida zuwa biliyan dari takwas ko wace shekara nan da shekarar 2030 mai zuwa.

Shi dai shirin bunkasa samar da makamashi ga kowa, an kaddamar da shi ne shekaru 2 da suka gabata, da manufar samar da makamashi ta hanyoyin zamani, da ninka ingancin makamashin da ake da shi, tare da samar da isasshen makamashi, musamman ga kasashe mafiya bukata. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China