Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Madam Hua Chunying ta bayyana a nan birnin Beijing a ranar laraba 14 ga wata cewa, wasu kungiyoyin 'yan ta'adda na yunkuri hada baki da reshen su a gida da na waje, domin cimma aniyar su na tada zaune tsaye a jihar Xinjiang ko sauran yankunan kasar Sin, game da wannan batu, gwamnatin kasar Sin na neman an san hakikanin fuskarsu da mugun nufin su. (Amina)