A halin yanzu, ana kidaya kuri'un da aka kada, kana bisa labarin da aka bayar, an ce, jam'iyyar ANC mai mulkin kasar ta samu goyon bayan kaso 61.83 bisa dari na masu kada kuri'un, haka kuma, babbar jam'iyyar adawa ta democratic coaliation ta samu goyon bayan kaso 24.07 bisa dari na masu kada kuri'un, yayin da jam'iyyar EFF ta samu goyon bayan kaso 4.56 bisa dari na masu kada kuri'un. Lamarin da ya sa aka yi hasashen cewa, babu tantama jam'iyyar ANC mai mulkin kasar za ta sake lashe babban zaben, amma farin jinin jam'iyyar ya ragu idan aka kwatanta da na shekarar da ta wuce da kaso 65.9 bisa dari.
Bugu da kari, za a bayyana sakamakon babban zaben a gobe Alhamis 8 ga wata da dare. (Maryam)