Kakakin ya ce, ban da shugabannin kasashen Najeriya, Chadi, Kamaru, Nijer, da kuma Benin, wasu wakilai daga kasashen Amurka, Burtaniya, da kuma kungiyar EU su ma za su halarci taron. Ya kuma kara da cewa, muddin ana fatan murkushe ta'addanci yadda ya kamata, dole ne a kara hadin kai tsakanin shiyya-shiyya da kasa da kasa, ta yadda za a iya musayar bayanai, da sa ido a kan iyakar kasashen juna. Ya kamata kasashen dake shiyyar su dauki babban nauyi wajen yaki da ta'addanci.
Har illa yau kakakin ya bayyana cewa, kasashen Afrika na fatan kara cimma matsaya da Faransa, da kuma samun goyon baya daga kasar da sauran kasashe a fannonin tsare-tsare da fasahohi. (Bilkisu)