in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yarjejeniyar tsagaita bude wuta a kasar Sudan ta Kudu ta fada ruwa
2014-05-12 11:14:01 cri

A ranar 11 ga wata da safe bisa agogon wurin, an yi musayar wuta mai tsanani a kewayen garin Bentiu na kasar Sudan ta Kudu, sojojin gwamnati da dakarun da ke adawa da gwamnati jim kadan bayan daddale yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin bangarorin biyu a Addis Abeba na kasar Habasha, wannan al'amari dai ya kawo illa ga kokarin da kasashen duniya suke yi wajen kawo karshen rikici a awannan kasa

A ranar 10 ga wata kuma, shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir da shugaban 'yan tawaye Machar sun gana tare da daddale yarjejeniyar tsagaita bude wuta, wadda ta bukaci bangarorin biyu da su tsagaita bude wuta kwata-kwata a cikin awoyi 24 bayan daddale yarjejeniyar. Wannan yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta kasance ta biyu da suka daddale, a watan Janairu na bana, bangarorin biyu sun taba daddale wata yarjejeniyar tsagaita bude wuta, kuma ba da dadewa ba, bangarorin biyu sun sake yi musayar wuta, abin da ya kawo rudani ga yarjejeniyar. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China