Bisa matakan da aka dauka daga dukkan fannoni, zabubukan kasar Afrika ta Kudu sun gudana yadda ya kamata, in ji hukumomin kasar a ranar Laraba.
Mutane sun je rumfunan zabe cikin wani yanayi na biki da zaman lafiya, duk da yawan dogayen layin mutane da aka samu a wasu yankunan kasar, in ji hukumar dake kula da ayyuka da samar da bayanai ta kasar NATJOINTS wadda aka dorawa nauyin kula da dukkan ayyukan tabbatar da tsaro da jami'an tsaro a cikin kasar.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar IEC ta rawaito cewa, wadannan zabubuka, an shirya su yadda ya kamata, kuma sun gudana cikin kwanciyar hankali.
Muna farin ciki ga yadda miliyoyin 'yan kasar Afrika ta Kudu suka halarci wannan zabe, kuma suka nuna natsuwa da sanin yadda ya kamata, in ji kakakin gwamnatin Afrika ta Kudu madam Phumla Williams.
Amma duk da haka, an samu korafe korafe da dama a cikin kasar, domin wasu jam'iyyun siyasa sun cigaba da rarraba kayayyaki irin su riguna da sauransu har cikin rumfunan zabe, lamarin da ya kasance laifi bisa dokokin zabe.
A dunkule, zabe ya gudana cikin lumana, kuma cikin nasara, amma kuma jami'an tsaro da wasu hukumomin gwamnati za su cigaba da sauraren korafe korafen da za'a gabatar wa hukumar IEC, ko wasu hukumomin kasar na daban, in ji madam Williams. (Maman Ada)