in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta samu wasu kudaden da za ta tallafawa 'yan gudun hijirar Sudan ta Kudu
2014-05-14 10:10:36 cri

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD UNHCR, ta ce, ta samu dala miliyan 6.8 da za ta taimaka wa 'yan gudun hijirar da ke zaune a jihohin Unity da Upper Nile da rikicin da ake yi a Sudan ta Kudu ya fi shafa.

Sai dai wakilin hukumar da ke kasar Sudan ta Kudu Cosmas Chanda, ya sake nuna damuwa game da halin da 'yan gudun hijirar ke ciki a yankuna da rikicin ya shafa, ganin yadda 'yan gudun hijirar ke dogaro kwacakwam kan tallafin daga ketare.

Jami'in ya ce, tun a shekarar da ta gabata, hukumar ta UNHCR da sauran abokan hulda suka bullo da wasu matakai, ciki har da kara daga matsayin tantunan wucin gadi a sassa daban-daban na kasar.

MDD ta yi gargadin cewa, idan har fadan ya ci gaba, rabin al'ummar kasar Sudan ta Kudu miliyan 12 za su rasa matsugunansu, ko su zama 'yan gudun hijira a kasashen ketare, ko su fuskanci yunwa, ko su mutu ya zuwa karshen shekara.

Alkaluma na nuna cewa, ya zuwa yanzu rikicin ya raba sama da mutane miliyan daya da gidajensu, ciki har da sama da mutane 80,000 da ke samun mafaka a sansanonin MDD da ke wurare daban-daban a kasar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China