Shugaba Zuma ya bayyana hakan ne jiya Asabar, bayan bayyana sakamakon babban zaben kasar na bana, zaben da ANC mai mulkin kasar ta lashe da gagarumin rinjaye.
Cikin jawabin da ya gabatarwa al'ummar Afirka ta Kudun, Mr. Zuma ya ce ANC za ta yi amfani da rinjayen ta, wajen aiwatar da manufofin da za su bunkasa rayuwar jama'a a dukkanin fannonin ci gaba.
Ya ce gwamnatin sa za ta ci gaba da daukar matakan samarwa al'ummar kasar ababen more rayuwa, da suka kunshi tsaftataccen ruwan sha, da hanyoyi, da lantarki, da inganta kiwon lafiya da ilimi da dai sauran su.
Sakamakon karshe da hukumar gudanar da zaben kasar mai zaman kanta IEC ta fitar dai ya nuna cewa, ANCn ce ke gaba da kaso 62.15 na daukacin kuri'un da aka kada, yayin da babbar jam'iyyar adawa ta DA ke matsayi na biyu da kaso 22.23 bisa dari na jimillar kuri'un. (Saminu Alhassan Usman)