MDD ta mika sakonta na taya murna ga al'umma da gwamnatin kasar Afrika ta Kudu, a game da nasarar da ta samu wajen gudanar da zabenta na majalisar dokoki da na larduna, a cikin kwanciyar hankali, duk kuwa da rahotannin da aka bayar wadanda ke nuni da cewar, an samu fitowar masu kada kuri'a da dama.
Wata sanarwa daga cibiyar yada labarai ta MDD dake Pretoria ta ce, babban sakatare na MDD Ban ki-moon ya yaba da kwazon Afrika ta Kudu a fafutukar da take yi na taka rawa da ta dace, a karkashin tsarin demokradiyyar kasar, wanda kasar ta yi gagarumar gwagwarmaya kafin ta girka tsarin a kasarta, a inda a wancan lokacin, shekaru 20 da suka shude, tun farko sai da ta gudanar da zaben farko na kasar, wanda ya kunshi jinsuna dabam-dabam na kasar.
MDD, a cikin sanarwa ta ce, ta yi amanna da cewar, za ta ci gaba da tallafawa Afrika ta Kudu, a kokarin da take yi na inganta adalci da ci gaba, domin amfanin dukanin bangarorin kasar.
A ranar Laraba ne Afrika ta Kudu, ta yi zabe domin zabar sabbin 'yan majalisa da kuma 'yan majalisa na larduna.
Afrika ta Kudun tana gudanar da zaben da ya kunshi dukanin jinsunan kasar, a karo na 5, tun bayan da aka kawo karshen mulkin wariyar na nuna bambancin launin fata a kasar a shekarar1994.
Hukumar zabe ta kasar Afrika ta Kudu mai zaman kanta IEC ta ce, alkaluma sun nuna cewa, adadin mutanen da suka kada kuri'un wannan zaben, shi ne adadi mafi yawa a cikin tarihin demokradiyyar kasar.
Shugaban hukumar zaben Afrika ta Kudu mai zaman kanta, Mosotho Moepya ya ce, ana sa ran an rigaya an kada kuri'u fiye da miliyan 18, a zaben kasar, kuma wannan shi ne adadi mafi yawa idan aka kwatanta da kuri'un da aka kada kuri'un miliyan 17.9 a shekarar 2009, da kuma kuri'u miliyan 15.5 da aka kada a zaben shekara ta 2004.
Ya ce, a daidai karfe shidan yamma, agogon Afrika ta Kudu, a jiya Alhamis, alkaluman sakamakon zaben sun nuna cewar, masu kada kuri'a miliyan 12.62 suka kada kuri'a. (Suwaiba)