Hakan a cewar shirin na WFP ya biyo bayan binciken baya bayan nan da ya nuna cewa fadace-fadace a kasar, na neman jefa al'ummun ta cikin bala'in yunwa.
Wata sanarwa da ofishin mukaddashin daraktan shirin WFP na kasar ya fitar a ranar Asabar, ta bayyana matukar bukatar da ake da ita, ta samar da damar shigar da agajin abinci da dubban mutanen dake cikin matsi kafin lokaci ya kuri. Kaza lika sanarwar ta bayyana ci gaba da tashe-tashen hankula a matsayin kalubale dake yiwa shirin na bada tallafin abinci tarnaki.
Wannan dai sanarwa na zuwa ne daidai lokacin da rahotannin bincike ke nuna matsanancin kamfar abinci da ake fuskanta, musamman a yankunan jihar Unity da rikicin kasar ya fi shafa. Yankunan da aka hakikance kaso 3 bisa 4 na al'umma na fuskantar karancin abincin.(Saminu Alhassan Usman)