in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban sakatare janar MDD ya yi maraba da cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Sudan ta Kudu
2014-05-10 16:51:35 cri
Babban sakatare janar na MDD, Ban Ki-moon ya yi maraba a ranar Jumma'a da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma tsakanin shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir da shuagan 'yan tawaye Riek Machar, tare da yin kira ga bangarorin biyu da suka dauki matakan gaggawa domin kawo karshen duk wasu tashe tashen hankali domin aiwatar da wannan yarjejeniya.

Sakatare janar ya gamsu da sanya hannu a ranar yau a birnin Addis Ababa, kan yarjejeniyar da za ta taimakawa ga warware rikicin Sudan ta Kudu, a cewar wata sanarwar da kakakin mista Ban ya fitar da ita a ranar Jumma'a da yamma a birnin New York.

Mista Ban na bukatar bangarorin da abin ya shafa da su aiwatar cikin gaggawa alkawuran da suka dauka, musammun ma tsagaita bude wuta.

Mista Kiir da Machar sun cimma yarjejeniya a ranar Jumma'a da safe, bayan wata tattaunawar keke da keke, a hedkwatar kasar Habasha, tun bayan barkewar yakin basasa a cikin watan Disamban da ya gabata. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China