Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya sanya wa wasu mutane biyar takunkumi kan rawar da suka taka a rikicin kasar jamhuriyar Afirka ta Tsakiya CAR.
Wata sanarwa da fadar Amurka ta White House ta fitar a ranar Talata, ta ce, shugaban ya sanya hannu kan wata dokar shugaba da ta amince da kakaba takunkumi kan mutanen biyar wadanda suka hada da tsohon shugaban kasar Francois Bozize, da Michel Djotodia, tsohon shugaban wucin gadin kasar, takunkumin da ya hada da rike kadarorinsu da kuma hana su duk wani tafiye-tafiye.
Mai magana da yawun fadar White House ta Amurka Jay Carney, ya ce, wannan wata manuniya ce cewa, babu wanda ya fi karfin doka ga duk masu kokarin kawo barazana ga zaman lafiya a kasar ta CAR.
Kasar Amurka ta yi kira ga dukkan bangarorin kasar, da su kawo karshen tashin hankalin da ke faruwa a kasar, tare da tabbatar adalci ga wadanda suka aikata laifuffukan take hakkin bil-adama, kana su yi aiki tare don samar da kyakkyawar makoma ga al'ummar kasar. (Ibrahim)