An shirya bikin sanya tauraron 'dan Adam kirar Fengyun na 3C da kasar Sin ta kera da kanta bisa hanyarsa a sararin samaniya a 'yan kwanakin baya a nan birnin Beijing. Kaddamar da yin amfani da shi, ya shaida cewa, fasahar tauraron 'dan Adam da ke binciken yanayi ta kasar Sin ta riga ta kai matsayin rukunin farko a duniya.
An ce, tauraron 'dan Adam lambar Fengyun na 3C zai bi hanyar watsa labaru kai tsaye dangane da yanayi, da hanyar bayar da hidimar kididdiga dangane da yanayi ga masaya. A sa'i daya kuma, zai samar da bayanai ga masayan duk duniya ta tsarin sadarwar duniya na kungiyar binciken yanayi ta duniya. A halin yanzu dai, yawan masayan da suka yi rajistar wajen yin amfani da tauraron 'dan Adam mai lambar Fengyun na 3 a gida da waje ya wuce dubu 20. (Danladi)