Wannan shi ne karo na biyar da ake gudanar da zaben majalisar dokokin kasar Afirka ta Kudu, tun bayan kawo karshen wariyar launin fata a shekarar 1994. Bugu da kari, wannan shi ne karo na farko da aka gudanar da zaben majalisar dokokin kasar tun bayan rasuwar tsohon shugaban kasar Nelson Mandela.
Bisa tsarin mulkin kasar Afirka ta Kudu, idan 'yan kasar Afrika ta Kudu suka zabi sabuwar majalisar dokokin kasa da farko, sa'an nan kuma, majalisar dokokin kasa ta zabi shugaban kasa a birnin Cape Town a ran 21 ga wata, a karshe a gudanar da bikin rantsar da shugaba da ministocin kasar a birnin Pretoria a ran 24 ga wata. (Maryam)