An bude sama da kashi 90 cikin 100 na cibiyoyin zaben kasar 22,360 da karfe 7 na safe, amma ba a bude wasu a kan lokaci ba saboda matsalolin kayan aiki da na ma'aikata.
Babban jami'in hukumar zaben kasar mai zaman kanta (INEC) Mosotho Moepya ya shaida wa manema labarai cewa, zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali da lumana a yankin Pretoria, sai dai an fuskanci zaman dar-dar a Bekkersdal da kudancin Johannesburg, bayan da aka kona wasu rumfunan zabe guda 2 ranar Talata da dare.
Sai dai kakakin gwamnatin kasar Phumla Williams ya sanar da cewa, an dauki matakan tsaro don tabbatar da cewa, an gudanar da zaben cikin lumana. (Ibrahim)