Kakakinr ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Madam Hua Chunying ta yi bayani game da ziyarar wakilin musamman na shugaban kasar Amurka kuma ministan kudin kasar Jacob Lew a gun taron manema labaru da aka saba yi a ranar laraba 14 ga wata, inda ta bayyana cewa, Sin da Amurka na da moriya bai daya fiye da bambancin ra'ayi dake tsakaninsu, kamata ya yi, bangarorin biyu sun tabbatar da bunkasa dangantakar dake tsakaninsu yadda ya kamata nan gaba. Madam Hua ya ce, Amurka na goyon bayan kasar Sin da ta jagorancikarbi bakuncinn babban kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar hadin gwiwa tsakanin kasashen dake yankin Asiya da tekun -Pacific kan tattalin arziki ta APEC.
Ban da haka kuma, Madam Hua ta bayyana cewa, shugabannin kasar Sin sun nuna cewa, kara hadin gwiwa tsakanin Sin da Amurka matakin da ya dace da moriyar bangarorin biyu ne baki daya, don haka Suna suna fatan kasashen za su tabbatar da matsaya daya da shugabanninsu suka daddale, da nacewa wajen kafa sabuwar dangantakar a tsakaninsu da ta dace. Spsannan kuma su hada kansu wajen yin shawarwari da mutunta moriyar juna, ta yadda za a ciyar da dangantakar dake tsakaninsu yadda ya kamata nan gaba. (Amina)